YADDA AKE GYARA MATACCEN MEMORY NA WAYA
A cikin sakonmu na baya TA YA ZAN ZAMA GWANI A COMPUTER mun gaya maka cewa za mu ci gaba da koya yadda za’a fara zama gwani (hacker) tare da CMD, wannan shine abin da za mu fara da shi
> Da farko zaka menu akan kwamfutarka sai kuma ka binciki CMD
> Sai ka danna Right click akan shi sai ka shiga Run as administrator ,
> Bayan ya bude, Rubuta diskpart sai ka danna enter
> sai ka rubuta List disk ka danna enter, wannan umarni zai nuna maka duk abin da ka Jona akan kwamfutarka
> sai ka zabi wanne memory ka jona,rubuta select disk 2
ka danna enter, ka tabbata ka duba ka fin selecting don zai iya zama disk 1 ko disk 0
> Rubuta Clean sai kai enter
> sa’an nan kuma rubuta waɗannan umurnai
> create partition primary sai kai enter
> select partition 1 sai kai enter
> active sai kai enter
jira wasu mintuna
> sai ka rubuta assign sai kai enter
sai zare memorin ka kara jonawa
duka duka wannan shine, idan kana da tambaya to rubuta a akwatin comment a kasa,